Ko kun san 'yan kwallon da suka mutu suna wasa?

Image caption Marigayi dan kwallon Kamaru Marc-Vivien Foé da ya mutu bayan da aka kai shi asibiti

Tun lokacin da aka kirkiro wasan kwallon kafa a duniya, ake samun 'yan wasan da suke mutuwa suna tsaka da murza leda.

Wasu 'yan wasan kuwa suna jin rauni ne a lokacin wasan da yake musabbabin mutuwar tasu.

Dan kwallon Staveley, William Cropper shi ne ya fara mutuwa a tarihin wasan kwallon kafa a ranar 13 ga watan Janairun 1989.

Staveley ya mutu a washe garin wasan da suka yi da Grimsby Town, bayan da ya samu karaya a kudunsa.

James Dunlop mai shekara 21, shi ne dan kwallo na biyu da ya mutu a tarihin wasan kwallon kafa, wanda ya buga wa St Mirren tamaula.

Dan wasan ya mutu ne a wasan sada zumunta bayan da ya fadi a kan gilas ya yanke shi, daga nan ne ya kamu da cutar Tetanus.

A ranar 12 ga watan Agusta dan wasan tawagar Nigeria, Samuel Okwaraji ya fadi ya mutu a filin wasa.

Okwaraji ya mutu ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a karawar da Nigeria ta yi da Algola.

Dan wasan tawagar Kamaru, Marc-Vivien Foé, shi ma ya mutu yana tsaka da wasa a ranar 26 ga watan Yunin 2003.

Vivien Foé ya mutu lokacin da yake buga wa Kamaru wasan Confederation Cup da Colombia, jim kadan da aka kai shi asibiti.

Sai dai kuma a cikin watan Mayun 2016 aka samu yan wasa hudu da suka mutu sanadiyyar wasan kwallon kafa.

A ranar 1 ga watan Mayun 2016, Stefan Petrovski mai wasa a Melaka United ya mutu a cikin filin wasa.

A kuma ranar 6 ga watan Mayun Patrick Ekeng dan kwallon Kamaru ya mutu a lokacin da yake buga wa Dinamo Bucureșt tamaula.

Shi kuwa dan wasan Bernardo Ribeiro mai shekara 26 ya mutu a ranar 7 ga watan Mayu yana yi wa Friburguense wasa.

Ta karshe karshensu ita ce Jeanine Christelle Djomnang mai tsaron ragar Kamaru, wadda ta mutu tana yin atisaye a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2016.

Jumulla 'yan wasa 129 ne suka mutu a tarihin wasan kwallon kafa a lokacin da suke tsaka da wasa ko kuma sanadiyyar rauni a wasan ya sa suka mutu.

Tuni hukumomin wasan kwallon kafa suka tsara matakan yin gwaje-gwaje domin kaucewa mutuwar 'yan kwallon ta dalilin wasa.