An ci kwallaye 467 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption Za a shiga wasannin mako na 25 a gasar ta Firimiyar Nigeria

An zazzaga kwallaye 467 a raga a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka buga wasanni 213.

Kungiyoyin da suka buga wasanninsu a waje sun ci kwallaye 121 a gasar da za a shiga mako na 25.

Godwin Obaje na Wikki Tourist da Okiki Afolabi na Sunshine Stars, sune ke kan gaba a yawan cin kwallaye, kowannansu ya ci 13.

Anthony Okpotu Lobi Stars da Isma'ila Gata na Ifeanyi Ubah suna matayi na biyu, inda kowannensu ya ci 10.

Wikki Tourist ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 41, yayin da Enugu Rangers ke matsayi na biyu da maki 39, sai Rivers United ta uku da maki 38 ma