Wales za ta kara da Belgium a gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wales da Belgium za su kara a wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin Turai

Tawagar kwallon kafa ta Wales da ta Belgium za su kece raini a wasan daf da na kusa da karshe a gasar nahiyar Turai a ranar Juma'a.

Wales ta kai wasan daf da na kusa da karshe ne, bayan da ta doke Ireland ta Arewa da ci daya mai ban haushi a wasan zagaye na biyu.

Ita kuwa Belgium ta kai wasan zagayen gaba ne, bayan da ta ci Hungary da ci 4-0.

Belgium ta samu nasara a karawa biyar daga fafatawa 12 da suka yi, Wales ta samu nasara a wasanni hudu suka buga canjaras a haduwa uku.

Faransa ce ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, an kuma fara buga wasannin daf da na kusa da karshe.