Bruce zai ci gaba da horar da Hull City

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Hull City za ta karbi bakuncin Leicester City a wasan farko a gasar Premier bana

Steve Bruce ya ce zai ci gaba da jan ragamar Hull City a kakar wasan kwallon kafa da za a fara a cikin watan Agusta.

Kocin wanda ya samar wa da Hull gurbin buga gasar da za a fara ta bana, ya kasa samun tabbaci daga mahukuntan kungiyar cewar za su yi tafiya tare.

Sai dai kuma Bruce, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce yadda ya sani kamar yadda aka saba ne, babu tabbas a kwallon kafa.

Ya kuma karyata batun da ake cewar mahukuntan kungiyar ba su ba shi damar sayo sabbin 'yan kwallo ba.

Hull City za ta karbi bakuncin Leicester City a wasan farko na gasar Premier a ranar 13 ga watan Agusta.