Man United zan buga wa tamaula - Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ibrahimovic ya buga wa Sweden gasar nahiyar Turai

Zlatan Ibrahimovic ya bayar da tabbacin cewar zai buga wa Manchester United tamaula a kakar wasan bana.

Yarjejeniyar Ibrahimovic mai shekara 34, ta kare ne da Paris St-Germain wadda ya buga wa wasanni tsawon shekara hudu.

Dan wasan zai murza-leda a Old Trafford karkashin Jose Mourinho, wanda ya horar da shi a Inter Milan.

Ibrahimovic ya rubuta a shafinsa na Instagram cewar, "Lokaci ya yi da zan sanarwa duniya cewar Manchester United zan buga wa tamaula.''

United wadda ta kare a mataki na biyar a kan teburin gasar Premier da aka kammala ba ta ce komai kan batun ba.