Hulk ya koma China a mafi tsada a tarihi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hulk ya yi wasanni da dama a China kafin ya koma Portugal

Dan wasan tawagar Brazil, Hulk, ya koma kungiyar Shanghai SIPG, da murza-leda a matsayin wanda aka saya mafi tsada a gasar China.

Hulk ya koma China da taka-leda kan kudi fam miliyan 46 da dubu 100 daga kungiyar St Petersburg.

Shanhai, wanda tsohon kocin Ingila ke jagoranta, Sven-Goran Eriksson ta karya tarihin sayen dan kwallon da Jiangsu Suning ta yi, inda ta sayi Alex Teixeira kan kudi fam miliyan 38 da dubu 400.

Hulk mai shekara 29 ya ci wa Zenith kwallaye 56 a gasar kwallon kafar Rasha da aka kammala a bana.

Dan kwallon ya buga tamaula a kungiyoyin China uku kafin daga baya ya koma Porto da wasa a shekarar 2008, daga nan kuma ya koma Zenith a shekarar 2012.

Hulk din zai taka leda a Shanghai ne tare da tsohon dan kwallon Sunderland, Asamoah Gyan.