Puel ya zama sabon kocin Southampton

Image caption Puel zai maye gurbin Koeman

An nada tsohon kocin Nice, Claude Puel a matsayin sabon Southampton.

Mista Puel, mai shekara 54, wanda ya bar Nice a watan Mayu bayan ya jagorance su zuwa mataki na hudu a teburin gasar Lig 1, ya sanya hannu a kwantaragin shekara uku a Southampton.

Ya maye gurbin Ronald Koeman, wanda ya zama kocin Everton ranar 16 ga watan Yunin nan.

Southampton ta so sayen tsohon kocin Roma Rudi Garcia, bayan yunkurin da ta yi na sayen tsohon kocin Manchester City Manuel Pellegrini bai yi nasara ba.

Eric Black, tsohon kocin-riko na Aston Villa, ya yi aiki da Puel a matsayin mataimakinsa.