Watford ta sayi dan wasan Liverpool Sinclair

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shi ne dan wasa na farko da Watford ta saya a bana

Kungiyar kwallon kafar Watford ta sayi dan wasan Liverpool Jerome Sinclair a wa'adin shekara biyar.

Sinclair, mai shekara 19, ya buga wa Liverpool kwallo sau biyar kuma ya zura kwallo a fitowarsa ta farko a wasan da suka yi da Exeter na cin kofin FA a watan Janairu.

Kungiyoyin biyu sun amince cewa Liverpool za ta barbi kusan £4m a kan dan wasan.

Shi ne dan wasa na farko da kungiyar ta saya kafin kakar wasa ta 2016-17.