Evans zai kara da Federer a gasar Wimbledon

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan Evans ya kai wasan zagaye na uku a gasar Wimbledon

Dan Evans zai fafata da Roger Federer a wasan zagaye na uku na gasar kwallon tennis da ake yi ta Wimbledon.

Evans ya kai wasan zagayen gaba ne a gasar, bayan ya doke Alexandr Dolgopolov da ci 7-6 (8-6) 6-4 6-1.

Evans zai buga wasan zagayen gaba da Federer wanda ya doke Marcus Willis.

A gasar US Open da aka yi a shekarar 2013, Evans ya taka rawar gani inda ya fitar da Kei Nishikori da Bernard Tomic kafin ya sha kashi a hannun Tommy Robredo.