Neymar zai ci gaba da murza leda a Barca

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta ce Neymar zai ci gaba da murza mata leda bayan ya sanya hannu a sabon kwantaragin shekara biyar.

Za a kara wa dan kasar ta Brazil kudi daga £167m zuwa £186m wadda za a ba shi a shekara biyun farko, sannan a ba shi £209m a shekara ukun karshe.

Rahotanni na cewa Manchester United da Paris St-Germain suna son sayen dan wasan mai shekra 24.

Neymar ya zura kwallo 55 a fitowa 93 da ya yi a wasan La Liga tun da ya koma kungiyar daga Santos a shekarar 2013 a kan £48.6m.

A ranar Alhamis, shugaban Barcelona Josep Bartomeu ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da dan wasan, kuma shi kansa Neymar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana "matukar farin cikin ci gaba da murza leda" a kungiyar.