Pato, Falcao da Marco Amelia sun bar Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty

Alexandre Pato ya bi sahun Radamel Falcao da Marco Amelia domin barin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Pato, dan kasar Brazil mai shekara 26, ya je Chelsea ne a matsayin aro daga Corinthians a watan Janairu, inda ya ci fenareti a wasansa na farko, wanda suka doke Aston Villa da 4-0 a watan Afrilu.

Mako daya bayan hakan, ya buga wasan da suka sha kashi a hannun Swansea da ci 1-0.

Falcao ya koma Monaco bayan wa'dinsa ya kare a Chelsea, yayin da Amelia, wanda ya ke kungiyar domin maye gurbin Thibaut Courtois amma bai buga wasa ba, ya kama gabansa.