Ryan Giggs zai bar Manchester United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ryan Giggs bai ji dadin korar Van Gaal ba

Shahararren dan wasan Manchester United, wanda ya shafe shekara 29 a kungiyar, Ryan Giggs, zai yi ritaya bayan an amince za a ba shi kudin sallama.

Ana sa ran nan da kwanaki kadan kungiyar za ta fitar da sanawa kan batun.

Saura shekara daya kwantaragin Giggs, mai shekara 42, a matsayinsa na mataimakin koci, ta kare, sai dai sabon koci Jose Mourinho yana shirin maye gurbin sa da dadadden abokinsa, Rui Faria.

Ba a sabunta kwamtaragin Giggs, wanda ya buga wa kungiyar kwallo sau 963 ba, don haka ne zai san inda dare ya yi masa.

Giggs ya mika dukkan kayayyakin aikinsa, kuma dama bai taba boye shirinsa na barin kungiyar ba.

An ce Giggs bai ji dadin yadda aka sallami tsohon kocin kungiyar Louis van Gaal ba.

Kazalika, Giggs bai ji dadin yadda aka ki nada shi a matsayin kocin kungiyar ba, inda aka nada tsohon kocin Chelsea ada Real Madrid Mourinho.

Giggs ya shiga makarantar koyon kwallon kafa ta United ne yana dan shekara 14, inda ya zama cikakken dan wasa a shekarar 1990 kuma ya fara murza leda a wasan da suka fafata da Everton a watan Maris na 1991.