Arteta zai fara horarwa a Man City

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arteta ya bugawa Arsenal tamaular shekara biyar

Tsohon dan wasan Arsenal, Mikel Arteta, ya karbi aikin koci a Manchester City, karkashin Pep Guardiola.

Arteta mai shekara 34, ya yi murabus daga buga kwallo a karshen kakar da aka kammala, bayan da ya bugawa Arsenal tamaula ta shekara biyar.

Dan kwallon ya lashe kofin kalubale biyu a Arsenal, inda ya buga mata wasanni 150, ya kuma ci kwallaye 17.

Arteta ya ce ya dade yana mafarkin ya zama kocin tamaula, ya kuma yi murna da ya samu damar da zai yi aiki tare da Guardiola.

Manchester City ta dauko tsohon kocin Barcelona, Pep Guardiola daga Bayern Munich, domin ya ja ragamar kungiyar a kakar wasannin bana.