An amince da tayin da United ta yi wa Mkhitaryan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Borussia ta amince Mkhitaryan ya koma Man U

Borussia Dortmund ta yadda da tayin da Manchester United ta yi wa Henrikh Mkhitaryan, domin ya koma Old Trafford da taka-leda.

Dortmund ta sayi dan was an dan kasar Armenia kan kudi fan miliyan 23 da dubu dari biyar a shekarar 2013, kuma a shekara mai zuwa yarjejeniyarsa za ta kare da kulob din.

Mkhitaryan, mai shekara 27, bai je Old Trafford domin a duba lafiyarsa ba, hasali ma ba a kammala kulla yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu ba.

Idan har ya koma United da wasa, zai zama dan kwallo na uku da kungiyar ta saya, bayan Erik Bailly da Zlatan Ibrahimovich.