Wimbledon: Serena ta kai zagaye na hudu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Williams za ta fafata ne da Svetlana Kuznetsova a zagaye na hudu

Serena Williams na kan hanyar lashe gasar kwallon tennis ta bakwai a tarihi, bayan da ta doke Annika Beck a wasan zagaye na uku.

Serena ta samu nasara ne da ci 6-3 da 6-0, wanda hakan ya sa ta kai wasan zagaye na hudu kenan a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Williams din za ta fafata a wasan gaba ne da Svetlana Kuznetsova, wacce ta doke Sloane Stephens 6-7 (1-7) 6-2 8-6 .

A ranar Litinin ake sa ran buga dukkannin wasannin zagaye na hudu a gasar ta Wimbledon.