U20: Nigeria za ta isa Sudan ranar Laraba

Image caption Amunike ya ce fafatawar ba za ta zo da sauki ba don tawagar Sudan ba kanwar lasa ba ce

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria, ta matasa ‘yan kasa da shekara 20, za ta ziyarci Sudan a ranar Laraba, domin karawa da tawagar kasar.

Kasashen biyu za su buga wasan zagayen karshe a neman gurbin shiga gasar cin kofin matasa ‘yan kasa da shekara 20 ta Afirka.

Kociyan tawagar Nigeria, Emmanuel Amuneke ya ce Sudan ba kanwar lasa ba ce, saboda haka wasan ba zai zo musu da sauki ba, amma yana fatan samun nasara a karawar.

Tawagar ta Nigeria ta buga wasannin sada zumunta sama da guda 20 tun lokacin da ta fara shirye-shirye a Abuja a ranar 9 ga watan Afrilu, inda ta yi canjaras a wasanni biyu, ta lashe sauran karawar.

Tun farko an tsara cewar kasashen biyu za su kara ne a ranar 8 ga watan Juli a Sudan, amma yanzu wasan ya koma ranar 10 ga watan Yuli.