Ahmed Musa na shirin komawa Leicester

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Musa ne kadai dan wasan da ya ci wa Najeriya kwallo sau biyu a wasan karshe na gasar cin kofin duniya

Kungiyar kwallon kafar da ta lashe gasar Premier Ingila ta bana, Leicester City, ta kulla yarjejeniya da CSKA Moscow domin sayen dan wasan Nigeria Ahmed Musa.

Wakilin dan wasan mai shekara 23, wanda ya koma CSKA 2012 sannan ya zura kwallaye 54 cikin fafatawa 168da ya buga, ya shaida wa BBC cewa Ahmed Musa na shirin sanya hannu a kwantaragin kungiyar.

Tony Harris ya ce, "An kammala komai kuma Musa zai tafi Ingila domin a yi masa gwajin lafiyarsa ranar Laraba."

BBC ta fahimci cewa Ahmed Musa ya ki tayin da kungoyin kwallon kafar Southampton, Everton da West Ham suka yi masa.

Kocin CSKA Moscow Leonid Slutsky ya amince cewa Ahmed Musa, wanda kan buga wasan tsakiya da na gaba, na shirin barin kungiyar.

A cewarsa, "Dan wasan zai bar kungiyar nan ranar Talata. Idan ka yi la'akari da yadda ake murza leda a Ingila, to lallai za ka ga cewa dan wasan zai fi dacewa da can."

Musa ya fara murza leda a kasashen duniya ne a kungiyar kwallon kafar Madagascar a shekarar 2010 kuma ya ci kwallaye 11 a wasa 58 da ya buga wa Super Eagles.

Sau biyu yana shan kwallo a wasan da Argentina ta doke Nigeria da ci 3-2 a gasar cin kofin duniya da aka yi a Barazil a shekarar 2014, inda ya zama dan wasan Najeriya na farko da ya zura kwallo biyu a wasan karshe na gasar cin kofin duniya.