Giggs zai yi fice a horar da tamaula — Ferguson

Image caption Sir Alex ya ce lokaci ya yi da ya kamata Giggs ya bar Man U

Tsohon kociyan Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce ya dace da Ryan Giggs, ya bar United, kuma yana da kwarewar da zai yi fice a horar da tamaula.

Zaman Giggs mai shekara 42, wanda ya yi shekara 29 a United ya zo karshe ne, bayan da sabon koci Jose Mourinho ya ce ba zai yi aiki tare da shi ba.

Ferguson ya ce Mourinho yana da damar da ya zabi aiki tare da tsohon mai taimaka masa Rui Faria, maimakon Ryan Giggs.

Tsohon kocin United, mai shekara 74, ya ce lokaci ne ya yi da Giggs zai ci gashin kansa, ya kuma rungumi kalubalen da zai fuskanta a fagen horar da tamaula a duniya.

Ya kuma kara da cewar Giggs yana da dukkan kwarewar da ake bukata a wajen mai horar da wasan kwallon kafa, saboda haka yana ganin zai yi fice a cikin aikin.