Manchester City ta sayi Zinchenko

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zinchenko ne dan wasa na hudu da City ta saya a karkashin jagorancin Pep Guardiola

Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta sayi dan wasan tsakiya dan kasar Ukraine Oleksandr Zinchenko daga FC Ufa.

Dan wasan, mai shekara 19, ya murza wa Ukraine leda a gasar cin kofin Turai ta bana, inda ya fafata a dukkan wasannin da kasar ta yi kafin a fitar da ita daga gasar.

Ukraine ta gaza zura kwallo a rukunin C, inda ta bar Jamus, ArewacinIreland da Poland suka ci karensu babu babbaka.

Zinchenko ne dai dan wasa na hudu da City ta saya a karkashin jagorancin Pep Guardiola, bayan ta sayi Ilkay Gundogan, Aaron Mooy da Nolito.