NFF za ta bayyana masu zawarcin Super Eagles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Salisu Yusuf ne kocin rikon kwarya na Eagles a yanzu

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF, ta ce za ta bayyana sunayen masu neman aikin horar da tawagar kwallon kafar kasar, wato Super Eagles a ranar 8 ga watan Yuli.

Shugaban kwamitin da aka bai wa zakulo kocin da zai ja ragamar Super Eagles, Barister Chris Green, ya ce tuni suka bai wa kowa damar mika takardun zawarcin aikin, domin a tantance wanda ya kamata ya karbi aikin.

Tawagar ta Nigeria tana hannun Salisu Yusuf a matsayin kocin rikon kwarya, wanda ya jagoranci Super Eagles ta doke Mali da Luxembourg a wasannin sada zumunta da suka fafata.

Nigeria tana rukuni na biyu tare da Algeria da Kamaru da Zambia a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2018 a Rasha, kuma kasa daya ce za ta wakilci Afirka a cikin wannan rukunin.

Chairman of the committee, Barrister Chris Green, told thenff.com that applications are invited from all persons who feel they are qualified for the position, as the three –time African champions get set to begin preparations for an interesting 2018 FIFA World Cup qualifying race against Algeria, Cameroon and Zambia.