Barcelona ta sake daukar Denis Suarez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Denis Suárez

Barcelona ta amince ta sake dawo da tsohon dan wasanta Denis Suarez, daga kungiyar Villareal.

Suarez mai shekara 22, ya saka hannu kan kwantiragin shekara hudu, da kuma yarjejeniyar za a iya tsawaita zamansa a Barca zuwa shekara daya.

Za a auna lafiyar tsohon dan kwallon Manchester City a ranar Talata, sai kuma a ranar Laraba ne Barcelona za ta sanar da kammala daukar dan wasan.

Suarez dan kwallon tawagar Spaniya, ya taimakawa Villareal ta kare a mataki na hudu a kan teburin La Liga da aka kammala a bana.