Na karbi aikin da kowa ke bukata – Mourinho

Image caption Morinho ya ce ya je kungiyar da yake burin yi wa aiki

Jose Mourinho ya ce yana da jan aikin gina Manchester United, ya kuma nanata cewar ya je kungiyar da yake son ya yi aiki.

Sabon kocin ya kara da cewar yana tunanin cewar aikin horar da United, kowa yana bukatar yi, kuma ba kowa ne zai samu damar hakan ba, amma an ba shi aikin.

Mourinho tsohon kociyan Chelsea, ya maye gurbin Louis van Gaal, wanda United ta kora, bayan da ya lashe kofin FA a cikin watan Mayu.

Mourinho ya ce ya yi takaici da United ba za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana ba, amma ya je kungiyar ne domin ya lashe kofuna.

United wadda ta dauki kofin Premier sau 20 a tarihi, ta kammala a mataki na biyar a gasar da aka kare ta bana.