An fitar da ‘yan wasan Firimiya da za su Spaniya

Image caption Shehu Dikko ne mataimakin hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta fitar da sunayen ‘yan wasa 32, wadanda za ta zabi 22 da za su je Spaniya buga wasannin sada zumunta.

Hakan ya biyo bayan hadin gwiwa da hukumar gasar Firimiyar Nigeria ta kulla yarjejeniya da ta gasar La Ligar Spaniya domin yin aiki kafada da kafada.

‘Yan wasan na gasar Firmiyar Nigeria za su kara da Valencia da kuma Malaga daga tsakanin 11 zuwa 13 ga watan Agusta.

An umarci ‘yan kwallon da aka gayyata da su halarci filin atisayen zagayen farko daga ranar 11 zuwa 18 ga watan Yuli.

Za kuma su sake yin atisaye zango na biyu a ranar 1 zuwa 8 ga watan Agusta, wacce ita ce ranar da za su ziyarci Spaniya.

Cikin wadanda aka bai wa goron gayyata sun hada da masu tsaron raga hudu da masu tsaron baya takwas da masu buga wasan tsakiya 10 da masu buga gefe bakwai da masu cin kwallaye shida.