Norwich za ta sayi Canos na Liverpool

Image caption Liverpool ta amince da tayin da Norwich City ta yi wa Sergi Canos

Liverpool ta amince da tayin da Norwich City ta yi wa Sergi Canos, kan kudi fan miliyan biyu da dubu dari biyar.

Matashin dan kwallon, wanda ya taka leda a karamar kungiyar Barcelona, ya buga wasanni aro a Brentford, inda ya ci kwallaye bakwai a wasanni 39 da ya buga.

Dan wasan tawagar Spaniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 19 , ya koma Liverpool a shekarar 2013, ya kuma buga wasan karshe a gasar Premier da aka kammala.

Canos zai maye gurbin Nathan Redmond a Norwich, wanda ya koma Southampton da murza-leda.