Nani ya kammala komawa Valencia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nani tsohon dan kwallon kungiyar Manchester United ne

Valencia ta dauki tsohon dan kwallon Manchester United, Nani daga kulob din Fernerbahce, amma ba a bayyana kudin da aka sayo shi ba.

Nani wanda ke buga wa Portugal gasar cin kofin Turai, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Valencia.

Dan kwallon wanda ya fara murza-leda a Sporting Lisborn, ya koma Fernabahce da taka leda daga Manchester United a shekarar 2015.

Nani wanda ya lashe kofunan Premier da na zakarun Turai a Old Trafford, ya buga wa Fernabahce wasanni 46 ya kuma ci mata kwallaye 12, bayan da kungiyar ta yi ta biyu a gasar Turkiya da aka kammala.