Berlusconi ya sayar da AC Milan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon Firaiministan Italiya, Berlusconi yana da magoya baya da yawa

Tohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi, ya ce ya sayar da Kulob din AC Milan ga wasu attajiran China.

Berlusconi, wanda ya mallaki kulob din da yake buga gasar Serie A, ya sanar da hakan a wata kafar yada labarai a ranar Talata.

Ya ce attajiran China za su biya fan miliyan 220 daga nan zuwa shekara biyu, wanda darajar kulob din ta kai kudi Yuro miliyan 750 har da bashin da ake bin sa.

Attajiran za su biya kashi 80 cikin dari cikin kankanin lokaci, sannan daga baya su sayi kason da ya rage.