Liverpool na son tsawaita zaman Klopp a Anfield

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp

Masu mallakar Liverpool sun yi wa kocin kungiyar, Jurgen Klopp, tayin kara tsawaita zamansa a Anfield.

Klopp mai shekara 49, ya koma horar da tamaula a Liverpool a cikin watan Oktoba, kan kwantiragi zuwa shekarar 2018, da kuma yarjejeniyar za a iya tsawaita ta zuwa shekara daya.

Liverpool na son tsawaita zaman kociyan a kungiyar, tare da fatan shi ne zai dawo da martabarta a fagen tamaula a duniya.

Klopp ya jagoranci Liverpool zuwa wasan karshe a League Cup, da kuma samun gurbin buga gasar Europa League a kakar wasan da aka kammala.

Kafin Klopp ya koma Liverpool, ya dauki kofuna biyu na gasar Jamus da kai wa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a Borussia Dortmund.