Man United ta dauki Henrikh Mkhitaryan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon dan wasan da Manchester United ta dauka, Henrikh Mkhitaryan

Manchester United ta kammala daukar dan kwallon tawagar Armenia, Henrikh Mkhitaryan daga Borrussia Dortmund.

Dan kwallon mai shekara 27, ya kulla yarjejeniyar shekara hudu, da sharadin za a iya tsawaita zamansa zuwa shekara daya, sai dai United ba ta fadi kudin da ta saye shi ba.

Mkhitaryan kyaftin din tawagar Armenia, shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da ya fi yin fice a Bundesligar Jamus da aka kammala, inda ya ci kwallaye 23 a kakar bana.

Dan kwallon ya yi wa Dortmund wasanni 140, ya kuma ci mata kwallaye 41, tun lokacin da ya koma can da murza-leda kan kudi fan miliyan 23 da dubu dari biyar a shekarar 2013.

.