Klopp ya tsawaita zamansa a Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klopp ya taka rawar gani

Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta tabbatar cewa kocinta Jurgen Klopp ya sanya hannu a sabon kwantaragi, wata tara bayan ya soma aiki da ita.

Yanzu dai za a tsawaita zamansa a kungiyar zuwa shekarar 2022.

Da ma dai a shekarar 2018 ne kwantaragin Klopp zai kare a kungiyar bayan ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu da rabi a kan £15m lokacin da ya maye gurbin Brendan Rodgers a watan Oktoban da ya wuce.

Sai dai mutanen da suka mallaki kungiyar ta Liverpool, Fenway Sports Group, sun fara tattaunawa da shi a kwanakin baya domin yiwuwar tsawaita zamansa a kungiyar.

Kungiyar ta wallafa a shafinta na intanet cewa "Yanzu ne ma muka fara hulda da shi."

Klopp ya jagoracin kungiyar ta Liverpool zuwa wasan karshe na cin Kofin Lig da Europa a kakar wasan da ta wuce bayan ya jagoracin Borussia Dortmund domin daukar kofuna biyu na Jamus.