Newcastle ta sayi Jesus Gamez

Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyar kwallon kafar Newcastle United ta sayin dan wasan Atletico Madrid, Jesus Gamez, domin yin wa'adin shekara biyu.

Dan wasan, mai shekara 31, wanda ya fi yin wasa a gefen dama, ya fito sosai a wasannin da Atletico Madrid ta yi a kakar wasan da ta wuce, inda ya buga mata wasa sau 16.

Jesus Gamez ya koma Madrid ne daga Malaga a shekarar 2014, bayan ya buga musu wasa sau 289 a kakar wasa tara.

Dan wasan ya ce, "wannan shi ne lokacin da ya yi daidai da na bar Atletico Madrid kuma matakin da na dauka yana da kyau. Zan yi bakin kokari na wajen ganin Newcastle ta koma kan ganiyarta a gasar Premier, kuma ina farin cikin zuwa nan. "

Gamez shi ne dan wasa na hudu da kocin kungiyar Rafa Benitez ya saya a lokacin bazara.

Benitez ya ce, "Benitez said: "Gamez dan wasan baya ne wanda zai iya murza leda daga kowanne bangare, dama da hagu. Yana da kwarewa, kuma na san shi a matsayin mai jarircewa."