Za a fara sauraren daukaka karar Blatter

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Baltter da Platini sun musanta zargin da ake yi musu

Kotu sauraren kararrakin wasanni, CAS, za ta fara sauraren daukaka karar da tsohon shugaban Fifa, Sepp Blatter ya yi zuwa gare ta a ranar 25 ga watan Agusta.

Kwamitin ladabtarwa na Fifa ne ya dakatar da Blatter da Platini daga shiga harkokin wasan kwallon kafa tsawon shekara shida.

A cikin shekarar 2015 aka samu Blatter, mai shekara 80, da Michel Platini da keta ka'idar aiki, inda ake zargin Blatter da biyan Platini kudin ladan aiki fan miliyan daya da dubu dari uku.

A cikin watan Mayu Platini ya ajiye aikinsa na shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, bayan da aka ki rage masa hukunci da aka yanke na dakatar da shi shekara shida.

Dukkansu sun karyata aikata ba dai-dai ba a hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa.

Daga baya kwamitin daukaka kara na Fifa, ya rage hukuncin zuwa shekara shida, kotun daukaka karar wasanni ta kuma rage hukuncin Platini zuwa shekara hudu.