Yusuf yana cikin masu zawarcin Super Eagles

Hakkin mallakar hoto nff
Image caption Wadannan su ne wadanda NFF za ta zabi kocin Super Eagles a cikinsu

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta bayyana sunayen masu horar da tamaula uku, domin fitar da wanda za ta bai wa aikin horar da Super Eagles.

Cikin masu horar da kwallon kafa ukun da ta bayyana sun hada da Salisu Yusuf da Tom Sainfiet da kuma Paul Le Guen.

Kwamitin da zai zabo kociyan ya ce sama da mutane 20 ne suka mika takardun neman aikin jan ragamar Super Eagles.

Wadanda suka nemi aikin sun hada da Giovanni Solinas da Hey Antoine da Mark Wotte, da Ernesto Paulo Calvinho da Dorian Marin da Miodrag Jesic da Perry Hansen da Ove Pedersen da Adebayo Lateef Kola da Sylvanus Okpala da Peter Ijeh da Vladimir Petrovic-Pizon da Lodewijk de Kruif da Kenichi Yatsuhashi da Bjorn Frank Peters da kuma Ricki Herbert.

Yusuf mai shekara 54, ya buga wa tawagar Nigeria ta matasa ‘yan kasa da shekara 20, ya kuma horar da El-Kanemi Warriors da Kano Pillars da kuma Enyimba.

Haka kuma ya yi aikin mataimakin kociyan Super Eagles har karo hudu, ya kuma ja ragamar tawagar ta Nigeria a kocin rikon kwarya.

Hakan ne ya samu damar doke Mali da Luxembourg a wasan sada zumunta da suka yi a karshen watan Mayu.

A ranar Litinin 18 ga watan Yuli ne, kwamitin zai gana da masu horarwa uku, inda zai bayyana wanda zai jagoranci tawagar ta Nigeria a wasanninta na gaba.