Dan kwallon Munich zai koma Southampton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pierre-Emile Hojbjerg

Mai buga wa Bayern Munich tamaula Pierre-Emile Hojbjerg ya isa kungiyar Southampton domin a duba lafiyarsa, da nufin komawa can da taka-leda.

Dan wasan mai shekara 20, dan kwallon tawagar Denmark, zai kulla yarjejeniya kan kudi fan miliyan 12 da dubu dari takwas.

Hojbjerg ya yi wasanni aro a Schalke a kakar da aka kammala, za kuma a sayar da shi ne, saboda sayen Renato Sanches da Bayern ta yi.

Bayern ce ta bayar da sanarwar cewar likitocin kungiyar Southampton za su duba lafiyar Hojbjerg a ranar Litinin.