Tore zai buga wa West Ham wasanni aro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tore zai buga wasa aro na tsawon shekara daya a West Ham

West ham United ta dauko dan kwallon Besiktas, Gokhan Tore, domin ya buga mata wasanni aro na shekara daya, da yarjejeniyar sayensa idan zama ya yi dadi.

Dan wasan Jamus da aka haifa a Turkiya, ya buga tamaula shekara biyu a karamar kungiyar Chelsea, ya kuma murza leda a Besiktas karkashin Slaven Bilic, kocin West Ham na yanzu.

Dan kwallon ya taimaka wa kungiyarsa doke Fernerbahce wajen lashe kofin kasar Turkiya da aka kammala.

Tore ya ci kwallaye hudu ya kuma taimaka aka zura shida a raga a wasanni 24 da ya buga wa Besiktas wacce ta lashe kofin Turkiya.