Shugaban Fifa zai gana da Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Muhammadu Buhari na son bunkasa harkar kwallon kafar Najeriya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, Gianni Infantino, zai gana da manyan jami'an hukumomin kwallon kafar Afirka a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta fitar, ta ce Mista Infantino zai isa Abuja ne ranar 24 ga watan nan na Yuli, inda zai gana da "shugabannin kungiyar kwallon kafar Afirka".

Infantino, wanda aka zaba a watan Fabrairun da ya wuce, zai samu rakiyar sabuwar Sakatare-Janar ta Fifa, Fatma Samoura.

Shugaban NFF Amaju Pinnick ya gana da Infantino inda suka tattauna a birnin Paris ranar Lahadi.

Shafin intanet na NFF ya ambato Pinnick yana cewa,"Shugaban Fifa da Sakatare-Janar za kuma su gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sannan su yi taro da shugabannin kungiyar kwallon kafar Afirka a lokaci guda."