Henry ya ki karbar aikin horar da Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thierry Henry ya ki karbar aikin horar da matasan kungiyar Arsenal masu shekara 18

Tsohon dan was an tawagar Faransa, Thierry Henry ya ki karbar aikin horar da matasan kungiyar Arsenal masu shekara 18.

Arsene Wenger ne ya yi Henry tayin aikin, amma ya bukaci da ya bar aikin sharhin tamaula da yake yi a gidan talabijin.

Sai dai Henry wanda ke rike da tarihin yawan ci wa Arsenal kwallaye, kuma mai takardar shaidar kociya ta hukumar kwallon Turai, bai amince ya bar sana'ar da ya ke yi ba.

Arsene Wenger zai bai wa tsohon kyaftin din Arsenal, Tony Adams, mai shekara 49, aikin horar da kungiyar matasan Arsenal.