'Kada ‘yan wasan Saliyo su yi batan dabo a Brazil'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tawagar 'yan wasan Saliyo

Tsohon dan kwallon tawagar Saliyo, Sheriff Suma, ya yi kira ga ‘yan wasan kasar da za su wakilce ta a wasannin Olympic da kada su yi batan dabo a Brazil.

Da akwai dadadden tarihin cewar ‘yan wasan Saliyo maza da Mata na guduwa daga sansanin da aka ajiye su, domin neman mafaka a kasar da suka je yin wasanni.

Shekara 13 da suka wuce Suma yana cikin ‘yan wasan kwallon kafar Saliyo ‘yan shekara 17 da aka yi gasar matasa a Finland, inda ‘yan kwallo 13 suka bazama cikin kasar.

Suma yana daga cikin ‘yan wasan Saliyo bakwai da suka koma gida, bayan da aka fitar da su daga gasar.

Daga baya ne Alimamy Sesay da kuma kyaftin din tawagar Saliyo na yanzu Umaru Bangura suka dawo kasar makwonni kadan da tserewar ta su.

Sauran kuwa sun ci gaba da neman mafaka a Finland da wasu kasashen Turai.