Tottenham ta dauki Janssen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janssen Shi ne dan kwallo na biyu da Tottenham ta sayo, bayan Victor Wanyama

Tottenham ta dauki Vincent Janssen daga AZ Alkamaar kan kudi fan miliyan 17, kan yarjejeniyar shekara hudu.

Dan wasan mai shekara 22, ya ci kwallaye 27 a gasar kasar Netherlands da aka kammala, ya kuma ci wa tawagar kasarsa kwallaye uku a wasanni biyar da ya yi.

Janssen Shi ne dan kwallo na biyu da Tottenham ta sayo, bayan Victor Wanyama da ta dauko kan kudi fan miliyan 11 daga Southampton.

Kungiyar Paris St-Germain ta Faransa da kuma Wolfsburg ta Jamus sun yi zawarcin Janssen a baya.