West Ham na zawarcin Bacca na AC Milan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Bacca ya ci wa tawagar kasarsa kwallaye biyu a gasar Copa America da aka kammala

West Ham United na tattaunawa da AC Milan kan batun daukar dan kwallonta Carlos Bacca.

Bacca mai shekara 29, ya koma AC Milan a kakar bara daga Sevilla kan kudi fan miliyan 21, ya kuma ci wa Milan kwallaye 21 a gasar Serie A ta Italiya.

Dan kwallon Colombia, ya ci wa tawagar kasarsa kwallaye biyu a gasar Copa America da aka kammala, inda suka kai wasan daf da karshe.

Tuni West Ham United ta dauki ‘yan wasa da suka hada daSofiane Feghoulida Havard NordtveitdaToni Martinez da kuma Gokhan Tore.