Allardyce zai zama kocin Ingila

Hakkin mallakar hoto PA

Sunderland ta amince da hukumar kwallon kafa ta Ingila da ta tattauna da Sam Allardyce, kan batun bashi aikin horar da tawagar kwallon kafar Ingila.

Ingila na neman kociyan da zai maye gurbin Roy Hodgson, wanda ya yi murabus daga aikin sakamakon fitar da Ingila daga gasar cin kofin nahiyar Turai da aka kammala.

Sunderlnad ta ce tana matukar kaunar Allardyce ya ci gaba da horar da kungiyar a kakar wasannin bana, domin yana da tsarin da zai kai su ga ci.

Bayan Allardyce, ana danganta kociyan Arsenal Arsene Wenger da na Bournemouth Eddie Howe da kuma na Hull City Steve Bruce, a matsayin wadanda hukumar kwallon Ingila za ta tattauna da su.