Willian ya tsawaita zamansa a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dan kwallon tawagar Brazil, Willian, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Chelsea zuwa shekara hudu.

Dan wasan wanda ya rage masa shekara biyu kwantiragin da ya kulla da Chelsea a baya ta kare, ya ci wa kungiyar kwallaye 13 a wasanni 59 da ya yi a bara.

Willian mai shekara 27, ya koma Chelsea daga Anzhi Makhachkala <http://www.bbc.com/sport/football/23814060> kan kudi fan miliyan 30 a shekarar 2013.

Jumulla Willian ya ci wa Chelsea kwallaye 19 a wasanni 140 da ya yi, kuma shi ne aka zaba a matsayin dan kwallon da yafi yin fice a kungiyar ta Chelsea