Ebola zai dambata da Shagon Buhari

Image caption Ebola da Shagon Buhari ne za su dambata

Bayan da Mai Takwasara ya doke Shagon Sawun Kura ranar Laraba, an raba Jadawalin zagaye na biyu a gasar mota ta jihar Kano.

'Yan damben Arewa hudu ne ke tsaye da suka hada da Shagon Buhari da Dan Bunza da Inda da Bahagon Sanin Kurna.

'Yan damben Kudawa biyu ne suka rage a gasar da suka hada da Shagon Mada da Ebola.

Guramada ma 'yan wasa biyu ne suka kai zagayen gaba a gasar.

Hakan ya sa aka kiya 'yan damben Arewa su yi zabe, nan ne Shagon Buhari ya dauko dambe da Ebola.

Danbunza kuwa da Habu Na Dutsen Mari ya zabo su dambata, yayin da Inda ya dauko Dogo Mai Takwasara.

Shi kuwa Bahagon Sanin Kurna da Shagon Mada zai dambata.

Mahukuntan gasar sun ce wasa biyu za a buga a ranar Alhamis tsakanin Shagon Buhari da Ebola da kece raini tsakanin Dan Bunza da Habu Na Dutsen Mari.

Sai kuma a ranar Asabar za a ci gaba da dambatawa tsakanin Inda da Mai Takwasara da kece raini tsakanin Bahagon Sanin Kurna da Shagon Mada.

A ranar Lahadi ake sa ran yin wasan karshe a kuma bai wa zakara motar hawa.