Za a shiga zagaye na biyu a damben gasar Mota

Dogo Mai Takwasara ya kai wasan zagaye na biyu a gasar da za a ci Mota, bayan da ya doke Shagon Tuwo na Arewa a turmin farko a ranar Talata.

A ranar ne kuma Habu na Dutsen Mari daga Guramada ya buge Shagon Bahagon Sarka daga Kudu a turmin farko.

Dogo Mai Takwasara na bangaren Guramda zai kara da Shagon Sawun Kura a ranar Laraba, daga nan ne za a fitar da jadawalin wasannin zagaye na biyu.

Ga jerin 'yan damben da ba su fadi ba

Bangaren Arewa: Inda Dan Nufawa da Dogon Bunza da Shagon Buhari da kuma Shagon Sanin Kurna.

Bangaren Kudawa: Ebola da Shagon Mada

Bangaren Guramada: Dogo Mai Takwasara da Habu na Dutsen Mari