‘Yan Firimiya da za su Spaniya sun fara atisaye

Nigeria ta fitar da sunayen 'yan wasa 32, wadanda za ta zabi 22 da za su je Spaniya buga wasannin sada zumunta.

Hakan ya biyo bayan hadin gwiwa da hukumar gasar Firimiyar Nigeria ta kulla yarjejeniya da ta gasar La Ligar Spaniya domin yin aiki kafada da kafada.

'Yan wasan na gasar Firmiyar Nigeria za su kara da Valencia da kuma Malaga daga tsakanin 11 zuwa 13 ga watan Agusta.

Bayan wannan atisayen, yan kwallon za su sake yin zango na biyu a ranar 1 zuwa 8 ga watan Agusta, wacce ita ce ranar da za su ziyarci Spaniyar.

Sauran 'yan wasan da suka isa sansanin sun hada da Ismaila Gata na Ifeanyiubah da Jamiu Alimi da kuma Ifeanyi Matthew dukkansu daga Kano Pillars.

Haka ma Sikiru Olatunbosun da Ifeanyi Ifeanyi 'yan wasan MFM FC da Okiemute Odah na Lobi Stars da 'yan kwallo Wikki Charles Henlong da kuma Al Hassan

Ibrahim suna cikin wadanda suka je sansanin horon.

Kelechi John na Plateau United da Shedrack Oghali na Warri Wolves da Gabriel Wassa na Niger Tornadoes da Ikechukwu Ezenwa na FC Ifeanyiubah da kuma Wassa and Ezenwa duk sun halarci sannin horo dake Abuja.