Nigeria ta koma ta 17 a iya tamaula a Afirka

Image caption A cikin watan Yuni Nigeria tana mataki na 61 a duniya

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria tana mataki na 17 a jerin kasashen da suka fi iya murza-leda a nahiyar Afirka a jerin da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fitar ranar Alhamis.

Nigeria wadda ke shirin nada sabon koci da zai jagoranci tawagar Super Eagles, tana mataki na 70 a jerin kasashen da suka yi fice a iya kwallon kafa a duniya.

A cikin watan Yuni Nigeria tana mataki na 61 a duniya, ta kuma samu wannan matsayin ne bayan da ta ci wasan sada zumunta da ta yi da Mali da kuma Luxembourg, wanda Salisu Yusuf ya jagoranci tawagar.

Har yanzu Algeria ce ke matsayi na daya a iya kwallo a Afirka sai Ivory Coast ta biyu, yayin da Ghana ke mataki na uku.

Sauran da suke biye da su sun hada da Senegal da Masar da Tunisiada Kamaru da Morocco da Jamhuriyar Congo da kuma Mali da suke cikin goman farko a Afirka.

Argentina ce ke matsayi na daya a duniya wajen taka-leda sai Belgium ta biyu, inda Colombia ce ta uku a jerin kasashen, Portugal wadda ta lashe kofin nahiyar Turai tana mataki na shida.