Skrtel ya koma Fenerbahce ta Turkiya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dan kwallon Liverpool, Martin Skrtel, ya koma Fenerbahce ta Turkiya da murza-leda, kan kudi fan miliyan biyar.

Skrtel kyaftin din tawagar Slovakia, ya buga wa Liverpool wasanni 319, tun lokacin da ya koma Anfield a shekarar 2008.

Dan wasan ya kuma nemi afuwar koci Jorgen Klopp kafin ya bar kungiyar, bayan da ya ci zarafinsa mai horarwa a kafar yada labarai.

Wani dan kwallon da ake sa ran zai bar Liverpoo, shi ne Mario Balotelli wanda Klopp ya shaidawa cewar ya nemi wata sabuwar kungiyar domin ba zai yi aiki da shi ba.