Ibrahimovic ba zai bi United China wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Morinho ba zai je atisaye da Ibrahimovic ba

Sabon kociyan Manchester United, Jose Mourinho, na shirin barin Ibrahimovich a gida, a lokacin da za su China wasannin atisaye tunkakar kakar bana a ranar Talata.

‘Yan wasan tawagar Ingila uku da suka hada da Wayne Rooney da Chris Smalling da kuma Marcus Rashford, suna cikin ‘yan wasan da United za ta je da su atisayen.

Sai dai kuma Mourinho ya ce ‘yan kwallon uku ba za su buga wasan sada zumunta da United za ta yi da Borussia Dortmund a Shanghai ranar 22 ga watan Yuli, da kuma karawa da Manchester City a Beijing ranar 25 ga watan na Yuli ba.

Yayin da Ibrahimovic mai shekara 34, ba ya cikin ‘yan kwallon da za su buga wa United wasannin atisayen A China.

Mourinho ya ce bai san lokacin da Ibrahimovic zai fara yi wa Manchester United wasan farko ba.