Shevchenko ya zama kocin Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ukraine ta nada tsohon dan kwallon AC Milan da Chelsea, Andriy Shevchenko a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafar kasar.

Shevchenko, mai shekara 39, ya buga wa Ukraine wasanni 111, zai kuma maye gurbin Mykhaylo Fomenko.

Fomenko ya jagoranci tawagar Ukraine shekara hudu, wadda aka fitar da kasar daga gasar nahiyar Turai a wasannin cikin rukuni.

Shevchenko shi ne mataimakin koci a karawar da kasar ta yi rashin nasara a hannun Jamus da Ireland ta Arewa da kuma Poland a gasar da aka kammala a Faransa.

Tsohon dan wasan Dynamo Kyiv wanda ya yi ritaya a shekarar 2012, bai taba yin aiki a matsayin mai horar da wata tawagar kwallon kafa ba.