Bounemouth ta dauki Jordan Ibe

Jordon Ibe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jordon Ibe ya bugawa Ingila wasa a rukunin matasa

Bournemouth ta kammala daukar dan kwallon Liverpool, Jordon Ibe bisa yarjejeniyar shekara hudu kan kudi fan miliyan 15.

Ibe mai shekara 20, ya yi wa Liverpool wasanni 58, tun lokacin da ya koma Anfield da murza-leda a shekarar 2011.

Dan kwallon ya buga wasannin Premier 12, ya kuma ci kwallo a karawar karshe da Liverpool ta yi da West Brom a gasar da aka kammala..

Ibe shi ne dan kwallo na biyar da Bournemouth ta saya a kakar bana.