An dage wasan da Eto’o ya gayyaci ‘yan kwallo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Eto’o ya shirya wasan ne tsakanin zakarun ‘yan kwallon duniya da kuma fitattu daga Turkiya

An dage wasan sada zumunta da tsohon dan kwallon tawagar Kamaru, Samuel Eto’o ya shirya za a yi a ranar Asabar a Turkiya.

An dage karawar sakamakon yunkurin juyin mulki da aka so yi a kasar, za kuma a sanar da ranar da za yi wasan nan gaba.

Eto’o ya shirya wasan ne tsakanin zakarun ‘yan kwallon duniya da kuma fitattu daga Turkiya, domin a tara kudin da za a taimakawa gidauniyarsa wadda ke tallafawa marasa gata.

Haka ma Marcel Desailly da Carles Puyol da Deco da kuma tsohon kociyan tawagar Ingila, Fabio Capello sun je Turkiyar don yin bikin da aka shirya na cikar gidauniyar Eto’o shekara 10 da kafuwa.